27 Afirilu 2020 - 07:26
Iran : Za a Fara Bude Wasu Wuraren Ibada

Shugaban Kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa za’a bude wasu wuraren addini a kasar, wadanda aka rufe su bayan bullar cutar corona watannin kimani 3 da suka gabata.

(ABNA24.com) Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Lahadi a lokacinda ya kai ziyarar aiki a cibiyar yaki da cutar ta Corona a ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar dake nan birnin Tehran.

Rouhani ya ce za’a raba kasar kashi ukku, gwagwadon yadda cutar corona ta yi barna a cikinsu da kuma yawan mace-macen da aka samu sanadiyar cuyar a yankunan.

Wuraren addinin da za’a buden hada da masallatai na jumma’a, masallatan salloli 5 da kuma waurare ziyara. Rouhani ya kara da cewa budewar za ta kasance daki-daki, gwagwadon yadda mutane ba zasu kamu da cutar Corona ba, tare da kiaye ka’idojin ma’aikatar lafiya na shiga wuraren.

Wannan dai shi ne mataki na farko wanda gwamnatin kasar Iran take dauka na bude wuraren ibada a kasar tun bayan bullar cotar Corona a kasar.



/129